Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe 'Yan Sanda 11 Da Sojojin NATO 2 A Kudancin Afghanistan


Jami'an Afghanistan sun ce 'yan tsageran Taliban sun kashe 'yan sanda 11 da maraicen jiya lahadi, yayin da sojojin NATO guda biyu suka rasa rayukansu a wani lamarin dabam a lardin Kandahar na kudancin Afghanistan.

Mukaddashin baturen 'yan sandan yankin, Amanullah Khan, ya ce 'yan Taliban sun bude wuta a kan wasu 'yan sanda dake barci a wani wurin binciken ababen hawa da mutane dake cikin lungu a gundumar Arghandab ta lardin Kandahar. Ya ce rahotannin farko sun nuna cewa daya daga cikin 'yan sandan yana da alaka da 'yan Taliban.

A halin da ake ciki kuma, ma'aikatar tsaron Britaniya ta ce mayakan saman kasar su biyu sun mutu a lokacin da motarsu ta taka nakiya. Rundunar NATO ta kuma ce wasu sojojin na Britaniya su biyu sun ji rauni a tashin wannan nakiya jiya lahadi.

Rundunar ta NATO ba ta bayyana zahirin inda wannan nakiya ta tashi ba.

Wannan farmaki shine na baya bayan nan da 'yan Taliban ke kaiwa kan 'yan sanda a kudancin Afghanistan. 'Yan Taliban din sun kashe 'yan sanda 8 ranar asabar a lardin Kandahar da kuma lardin Helmand dake makwabtaka da ita.

XS
SM
MD
LG