Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Benedict Yana Ziyarar Fadar White House


Shugaba Bush yana tarbar Paparoma Benedict yau laraba a fadar White House. Ana sa ran cewa baki dubu tara ne zasu gaida Paparoman a fadar White House a wannan rana da yake bukin cika shekaru 81 da haihuwa.

Irin wannan gagarumin bukin da aka shirya a fadar White House na ba-sabam ba ne ga wani bako, kuma wannan shine karo na biyu kacal a tarihi da wani Paparoma ya ziyarci fadar White House.

A bayan bukin, shugaba Bush da Paparoman zasu tattauna a ofishin shugaban. Daga baya kuma, Paparoman zai yi jawabi ga manyan fada na cocin Roman Katolika su 300 a babbar cocin Roman katolika ta nan Washington.

A lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa nan Washington, Paparoman ya bayyana kunyar da ya ji dangane da abin fallasar nan ta yadda wasu limaman cocin suke yin lalata da yara a nan Amurka. Cocin ta biya akalla dala miliyan dubu biyu ga wadanda aka yi ma lalatar an kuma cire daruruwan limamai daga mukamansu.

XS
SM
MD
LG