Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama Yace Yana Dab Da Zamowa Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar Democrat A Amurka


Mai neman jam'iyyar Democrat ta tsayar da shi takarar kujerar shugabancin Amurka, Barack Obama, ya ce yana dab da zamowa dan takarar jam'iyyar.

Obama yayi jawabi ga magoya baya yau laraba a Jihar Florida dake kudu maso gabashin nan Amurka, kwana guda a bayan da ya lashe zaben fitar da gwani a Jihar Oregon, ya gusa ga wakilai kasa da dari daya kawai domin tabbata a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat.

Mutum yana bukatar wakilai dubu biyu da ashirin da shida don zamowa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat.

Obama yayi kokarin sassauto da damuwar da ake yi cewar kiki-kakar da suke yi da Uwargida Hillary Clinton wajen neman tsayawa takarar na raba kan 'yan jam'iyyar, yana mai fadin cewa dukkan 'yan Democrat zasu hada kai don su doke dan takarar jam'iyyar Republican, John McCain, a babban zaben watan Nuwamba.

Amma Uwargida Clinton, wadda ita ma ke yakin neman zabe a jihar ta Florida ta ce kan jam'iyyar ba zai hadu ba har sai an kidaya da wakilan jihar. A ranar talata, ta samu nasara da gagarumin rinjaye kan Obama a Jihar Kentucky, amma wannan nasarar ba zata tabuka mata wani abin kirki ba wajen kamo kafar Obama, wanda yayi mata fintinkau a yawan wakilai.

Uwar jam'iyyar Democrat ta kasa ta kwace kujerun wakilan jihar Florida da na Jihar Michigan a saboda sun keta ka'idojin jam'iyyar ta hanyar gudanar da zabubbukan fitar da dan takararsu da wuri.

Uwargida Clinton ta ce tilas ne a kidaya kuri'un jihohin biyu kamar yadda aka kada su don tabbatar da cewa ana yin dimokuradiyya a lamarin.

XS
SM
MD
LG