Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakokin Aminu Ladan Abubakar, Alan Waka, Su Na Yin Kasuwa Sosai


Ban san ko mai karanta wannan labarin ya taba jin wata waka mai suna "Daurin Gwarmai" ko kuma wata mai suna "Bara A Kufai" ba, amma na san cewa zai yi wuya a ce mai sauraro bai ji wakar nan da ake kira "Jami'a Gidan Ban Kashi" ba. Idan kuwa ka ji wannan waka, to lallai ka ji wakar Aminudeen Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da sunan Aminu Ala, ko Alan waka.

Ni dai na jima da jin wasu wakokin Aminu Ala, amma Allah da ikonSa, kwanakin baya sai ga mu a gidan telebijin na CTV a Kano, inda muka taras da Aminu Ala yana waka tare da Maryam A. Baba da Fati Nijar.

Daga bisani, mun gayyaci Aminu Ala zuwa ofishin Muryar Amurka dake Kano, inda ya tattauna da filin "A Bari Ya Huce..." dangane da salon wakokinsa da kuma yadda ya fara yin waka.

Domin jin kashin farko na tattaunarmu da Aminu Ala a filin "A Bari Ya Huce...", sai a matsa rubutun dake saman wannan labarin. Idan kuma ana son jin samfurin wakarsa ta "Daurin Gwarmai" ana iya matsa inda aka rubuta hakan shi ma a saman wannan labarin. A kuma kasance da mu cikin makonnin dake tafe yayin da zamu kawo muku cikakkiyar hirar ta mu da Alan Waka.

XS
SM
MD
LG