Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kolin Kasashen Afirka yayi Kiran Da A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Zimbabwe


Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta amince da wani kuduri wanda yayi kiran da a kafa gwamnatin hadin kan kasa a Zimbabwe, a bayan zaben da aka yi ta tofin Allah tsine kansa na shugaba Robert Mugabe. Haka kuma shugabannin kungiyar dake ganawa cikin sirri a Masar, sun bukaci da a ci gaba da shiga tsakanin gwamnatin Zimbabwe da 'yan hamayyar kasar.

Talata aka amince da wannan matakin a bayan da kasar Botswana ta gabatar ad wata sanarwa mai zafin lafazi wadda ta nemi da a kori Zimbabwe daga tarurrukan Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da na Kungiyar Raya Kasashen Kudancin Afirka. Mataimakin shugaban Botswana, Mompati Merafhe, ya ce zaben fitar da gwani na makon jiya a kasar Zimbabwe bai tabbatar da halalcin gwamnatin shugaba Robert Mugabe ba.

Jami'an diflomasiyya a taron da aka yi cikin sirri, sun ce su ma shugabannin kasashen Nijeriya da Liberiya da Saliyo sun yi magana da lafazi mai karfi kan rashin halalcin zaben na Zimbabwe.

Wani kakakin gwamnatin Masar, Hossam Zaki, ya ce shugaba Mugabe yayi jawabi mai tsawo lokacin taron, inda ya fito da kakkausar harshe sukar kasashen Afirka da suka soki lamirinsa.

Tun fari talatar nan, shugabannin jam'iyyar hamayya ta MDC da na jam'iyyar ANU-PF mai mulkin kasar sun nuna cewa ba su da sha'awar ci gaba da tattaunawar siyasa. A cikin wata sanarwar da aka bayar a Harare babban birnin kasar, sakatare janar na jam'iyyar MDC, Tendai Biti, ya ce zaben bogi da aka ce an gudanar ranar 27 ga watan Yuni ya kawar da duk wata damar zaunawa don warware rikicin siyasar Zimbabwe.

Shi ma da yake magana a wurin taron kolin Kasashen Afirka a Masar, kakakin shugaban Zimbabwe, George Charamba, yayi watsi da kiraye-kirayen kafa gwamnatin hadin guiwa irin wadda aka yi a kasar Kenya, yana mai fadin cewa ai Zimbabwe ba Kenya ba ce.

XS
SM
MD
LG