Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Zata Fara Taron Koli Yau Litinin


Shugabannin kasashen Afirka da dama su na hallara a Sharm-el-Sheikh a kasar Misra, domin taron koli na 11 na Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da za a fara nan gaba a yau litinin.

Daftari na ajandar taron ya nuna cewa taken da za a maida hankali kai a bana shi ne cimma gurin samar da ruwan sha mai kyau da wuraren sarrafa najasa a nahiyar.

Amma kuma ana sa ran cewa halin da ake ciki a kasar Zimbabwe, inda a jiya lahadi aka rantsar da shugaba Robert Mugabe a bayan zaben da kusan kowa ya bayyana a zaman na bogi, shi ma zai dauki hankalin wannan taron koli.

Manyan jami'an diflomasiyya da 'yan siyasar Afirka sun gana cikin sirri na sa'o'i da dama cikin daren lahadi har zuwa asubahin litinin domin tattauna yadda za su takali irin barazanar da Mr. Mugabe yake yi wa mulkin dimokuradiyya.

Daya daga cikin kalubalen dake fuskantar Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka a yanzu shi ne ko za a amince da Mr. Mugabe a matsayin shugaban kasar Zimbabwe na halal. Ministan harkokin wajen Tanzaniya, ya ki yarda yayi sharhi a kan ko me kungiyar za ta yi.

Babbar jami'ar diflomasiyyar Amurka mai kula da harkokin nahiyar Afirka, Jendayi Frazier, ta yi magana a gefen taron kolin. Ta lura cewa 'yan kallo na kasashen Afirka ma sun yarda cewar zaben na kasar Zimbabwe bai kai mizanin da zai iya zamowa na gaskiya ba.

XS
SM
MD
LG