Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 15 Sun Mutu, 150 Sun Ji Rauni A Hare-Haren Bam A Istanbul A Kasar Turkiyya


Hukumomin Turkiyya sun ce mutane akalla 15 sun mutu, wasu 150 suka ji rauni a hare-haren bam guda biyu a birnin Istanbul.

Bama-baman sun tashi 'yan mintoci kadan a tsakanin juna jiya lahadi da maraice a kan wani titi na gidajen dake da kantuna a wata unguwa mai suna Gungoren a bangaren yammacin Istanbul.

Jami'ai suka ce bam na farko ya tarwatsa wani dakin yin wayar tarho, abinda ya janyo hankalin mutanen da suka taru don kallo. daga nan ne bam na biyu mai karfin gaske ya tashi. An boye dukkan bama-baman guda biyu a kwandunan shara.

Shugaba Abdullahi Gul na Turkiyya yayi tur da harin, ya kuma bayyana wadanda suka kai shi a matsayin 'yan ta'adda marasa imani. Hukumomi su na binciken ko su wanene suka kai harin.

A can baya, kungiyoyi da dama sun sha kai hare-hare a birnin Istanbul, ciki har da Kurdawa 'yan aware, da 'yan ra'ayin gurguzu da kuma masu kishin Islama.

XS
SM
MD
LG