Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Steve Lucas Yayi Ban Kwana Da Muryar Amurka


A bayan da ya shafe shekaru 24 a nan Muryar Amurka, Steve Lucas yayi ban kwana da wannan gidan rediyo. Ma'aikatan Sashen Hausa ba su bar shi ya tafi haka ba, domin kuwa sun shirya masa wata babbar liyafar da ta samu halartar shugabannin sassa da dama, da darektar Afirka da kuma darektan shirye-shirye na Afirka.

Shi dai Steve Lucas ya fara aiki da Muryar Amurka a matsayin mai labaran Hausa. Daga nan ya zamo shugaban Sashen Hausa, ya kuma zamo shugaban Sashen Afirka baki daya. An nada Steve Lucas darektan ofishin hulda da gidajen rediyon Afirka.

Kafin ritayarsa kuwa, shi ne darektan ofishin hulda da gidajen rediyon duniya na Muryar Amurka. Ofishin ya shirya masa wata liyafar ban kwana a ranar talatar makon jiya. A ranar larabar wannan makon kuma, Sashen Hausa ya karrama Steve Lucas da maidakinsa Fatouma da sauran iyalinsa a lokacin wata liyafar da ta hada da mika masa lambar yabo a zaman daya daga cikin jigogin kafawa da bunkasar Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Shugaban Sashen Hausa, Sunday Dare, ya yaba ma Steve a zaman mai basira da hangen nesa, wanda har bayan barinsa Sashen Hausa ya ci gaba da taimakawa da yin amfani da kwazonsa wajen ganin ci gaban Sashen.

Ita ma tsohuwar fardusar Sashen hausa, Donnie Butler, wadda ta yi ritaya a 'yan shekarun baya, ta yiwo tattaki musamman domin ta bayyana irin karimcin Steve Lucas da yadda ya rike mutane hannu bibbiyu a Sashen Hausa. Donnie Butler ta yi jawabi mai sosa zuciya kan irin kewar da ita da sauran wadanda suka yi aiki tare da Steve Lucas zasu yi na barinsa aiki.

Shirin "A Bari Ya Huce..." na wannan asabar, ya kunshi tattaunawa da Steve Lucas tare da maidakinsa Fatouma a kan shawararsu ta yin ritaya da kuma irin abubuwan da zasu yi nan gaba. Wakilin Sashen hausa na farko, Sani Abdullahi Tsafe, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa cikin shirin a kan halayyan dattaku na Steve Lucas.

Babu shakka, dukkanmu a nan Sashen Hausa za mu yi kewar Steve Lucas, amma da yake Nijar zai koma ya zauna, mun san cewa in sha Allahu ba ganin karshe ba ke nan da shi.

XS
SM
MD
LG