Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuri'un Neman Ra'ayoyin Jama'a Sun Nuna Barack Obama Na Jam'iyyar Democrat Yana Kan Gaba...


Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat a nan Amurka, Barack Obama, yana ci gaba da yin fintinkau ma abokin hamayyarsa, John McCain na jam'iyyar Republican, a kuri'un neman ra'ayoyin jama'a, yayin da 'yan takarar biyu suke yakin neman zabe a rana ta karshe kafin babban zaben da za a yi gobe talata.

Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a na baya-bayan nan sun nuna cewa Sanata Obama ya ba Sanata McCain ratar akalla maki 7. Wani dandalin tattara bayanan siyasa (RealClearPolitics.com) yayi hasashen cewa Obama yana iya samun isassun wakilan da za su ba shi kujerar shugabancin Amurka a zaben na gobe talata, abinda zai sa ya zamo bakar fata na farko da zai shugabanci Amurka.

A tsarin zabe na Amurka, kowace jiha tana da wakilai masu zaben shugaban kasa daidai yawan jama'arta da kuma wakilanta a majalisar dokokin tarayya. Kafin dan takara ya zamo shugaban kasa, sai ya samu akalla wakilai 270 daga cikin wakilai 538 masu zaben shugaban kasa.

Sanata McCain ya shirya kai ziyara zuwa jihohi har 7 a yau litinin. Ya fara da yin gangami a Jihar Florida, daga nan ya zarce zuwa Tennessee, zai kuma kammala da wani gangami a jiharsa ta Arizona da karfe 12 na dare. A yanzu dai, McCain yana kokari ne ya kare jihohin da 'yan Republican suka saba lashewa, wadanda a bana, Obama yake nuna alamun zai kwato.

Sanata Obama, yana gangami yau litinin a jihohi uku. Ya riga ya gudanar da taro a Jihar Florida, sannan zai ziyarci jihohin Carolina ta Arewa kafin ya zarce zuwa Virginia. Dukkan jihohin uku jam'iyyar Republican ce ta lashe su.

XS
SM
MD
LG