Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Majalisar Dinkin Duniya Ta Samu Tsohon Hafsan Sojan Rwanda Da Laifin Kisan Kare-Dangi


An yanke hukumcin daurin rai da rai a kan wani tsohon kanar na sojojin Rwanda a saboda rawar da ya taka wajen kashe-kashen kare-dangi na 1994.

Kotun Bin Bahasin Manyan Laifuffuka Ta Rwanda wadda Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, ta samu Theoneste Bagosora da aikata laifuffukan yaki, kisan kare-dangi da kuma cin zarafin bil Adama.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Bagosora a zaman daya daga cikin manyan wadanda suka kitsa, suka kuma rura wutar kashe-kashen kare-dangi na 1994 inda aka hallaka mutane kimanin dubu dari takwas.

A yaui alhamis ne kotun dake da zama a kasar Tanzaniya ta yanke hukumcin cewa Bagosora shi ne ya kitsa karkashe 'yan kabilar Tutsi a kewayen Kigali, babban birnin Rwanda, da kuma a birnin Gisenyi a lokacin da aka fara wannan fitina.

Har ila yau, kotun ta dora masa alhakin kashe sojojin kiyaye zaman lafiya 10 'yan kasar Belgium, da 'yan siyasar Rwanda da dama, cikinsu har da tsohuwar firayim minista Agathe Uwilingiyamana.

An samu wasu tsoffin hafsoshin soja biyu su ma da laifin kisan kare-dangi aka yanke musu hukumcin daurin rai da rai. Amma kotun ta wanke ta sallami tsohon Janar Gratien Kabiligi a saboda ba ta same shi da laifin komai ba.

XS
SM
MD
LG