Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Ruwan Yakin Kasar Sin Sun Doshi Yankin Ruwan Somaliya


Jiragen ruwan yaki guda uku na kasar Sin sun doshi yankin ruwan teku dake kusa da Somaliya domin shiga cikin jiragen kasashen waje dake yakar ‘yan fashi cikin teku da suke cin karensu babu babbaka.

A yau jumma’a jiragen kai farmaki guda biyu da wani jirgin mai dauka musu kaya suka bar sansaninsu a tsibirin Hainan na kudancin Sin domin yin sintiri a mashigin ruwan Aden da tekun Indiya. Jiragen su na dauke da sojoji akalla 800, cikinsu har da zaratan sojojin kasar ta Sin.

‘Yan fashi cikin teku na Somaliya sun sace jiragen ruwa fiye da arba’in a wannan shekarar, kuma a yanzu haka su na rike da jiragen ruwa akalla 15 tare da ma’aikatansu. A farkon watan nan, an kai farmaki a kan wani jirgin ruwan kasar Sin, amma ma’aikatansa sun samu nasarar korar ‘yan fashin.

A makon jiya, Kwamitin Sulhun MDD ya jefa kuri’ar bada gwamnatocin kasashen waje iznin shiga cikin yankin kasar Somaliya ta sama ko ta kasa domin farautar ‘yan fashin

XS
SM
MD
LG