Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawakan Kungiyar Firqatul Sahwa Sun Yi Mummunan Hatsarin Mota


'Yan kungiyar mawakan nan ta "Firqatul Sahwa" sun yi mummunan hatsari a bayan da suka bar wani gari mai suna Kosti-Rabak a kasar Sudan.

Dan jarida mai zaman kansa a kasar Sudan, Salman al-Parisi, ya fadawa filin "A Bari Ya Huce..." cikin wata hira ta musamman cewar wannan hatsarin mota da ya faru cikin dare ya girgiza hukumomi a Sudan, har ma a yanzu ta haramta yin tafiye-tafiye cikin mota da daddare.

Malam Salman ya ce wadanda suka mutu a wannan hatsari sun hada har da Awad Rashid Ahmad, da al-Ma'sum Umar da kuma Zain al-Abidin al-Sheikh. Daga cikin mawaka hudun da suka yi fice a wannan kungiya ta Firqatul Sahwa, mutum guda ne ya tsira da ransa, at-Tarefi Ahmad, dan'uwan Awad Rashid Ahmad.

Dan jaridar ya ce sanarwar farko da ta fito daga garin al-Zariba, hedkwatar marigayi Sheikh Abdul-Rahim al-Bura'i, ta bayyana cewa an yi mummunan hatsari ne, har ma wasu mawaka sun rasu, amma ba a bayyana sunayen wadanda suka rasu ba, sai bayan kwanaki uku.

Malam Salman al-Parisi ya ce 'ya'yan kungiyar ta Firqatul Sahwa sun je su garin Kosti-Rabak ne domin bukin auren wani dan'uwansu. A bayan da suka baro wurin wannan bukin ne cikin dare sun kama hanyar tafiya, sai wata motar tanka ta mai ta bugi motar da suek ciki ta baya, dab da garin Amr Wab.

Domin sauraron kashin farko na hirar da muka yi da Salman al-Parisi, sai a matsa alamar sauti dake sama, a hannun dama.

XS
SM
MD
LG