Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Ba Da Umurnin Dakatar Da Dukkan Shari'a A Kotun Soja A Guantanamo


Wani alkalin soja na Amurka ya dakatar da shari'ar da ake yi a gidan wakafi na sansanin sojan Amurka dake Guantanamo a tsibirin Cuba, ta mutane biyar da ake tuhuma da kulla makarkashiyar hare-haren ta'addancin ranar 11 ga watan Satumba da aka kai ma Amurka.

Wannan matakin da alkalin ya dauka yau laraba ya biyo bayan umurnin da shugaba Barack Obama ya bayar ga sakataren tsaron Amurka, Robert Gates, a kan a umurci masu gabatar da kararraki su shigar da takardun neman dakatar da dukkan shari'un da ake gudanarwa a sansanin na tsawon akalla kwanaki 120.

Shugaba Obama ya bada wannan umurnin 'yan sa'o'i kadan a bayan da aka rantsar da shi.

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi marhabin da wannan matakin na dakatar da shari'a a kotunan soja. A cikin wata sanarwar da ta bayar, hukumar shari'a ta Tarayyar Turai ta ce ta yi farin ciki sosai cewar daya daga cikin matakan farko da Mr. Obama ya fara dauka a matsayinsa na shugaban Amurka, shi ne kokarin kawo karshen wannan abin takaici.

Dakatar da shari'ar zata ba gwamnatin Obama lokaci na nazarin zargin da ake yi ma kowane daya daga cikin mutanen da ake tuhuma da ta'addanci, da kuma sake nazarin tsarin kotunan sojan baki dayansa.

Mr. Obama ya yi alkawarin rufe wannan gidan wakafi na Guantanamo wanda ake sukar lamirinsa.

XS
SM
MD
LG