Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Tsaron Nijar Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Kin Jinin Tazarce A Dosso


Dakarun tsaro a Jamhuriyar Nijar sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa 'yan zanga-zangar da suke yin Allah wadarai da yunkurin shugaba Mamadou Tandja na sauya tsarin mulkin kasar domin ya nemi wa'adi na uku a kan karagar mulki.

Shaidu sun ce dakarun sun kutsa don tarwatsa taro a bayan da masu zanga-zanga suka lalata gine-ginen gwamnati da motoci jiya litinin a garin Dosso, mai tazarar kimanin kilomita 140 a kudu maso gabas da Yamai, babban birnin kasar.

A bisa tanadin da tsarin mulkin Nijar yayi, shugaba Tandja zai sauka daga kan mulki a karshen wa'adinsa na biyu a watan Disamba, amma kuma yace yana son a yi kuri'ar raba-gardama domin a kawar da wannan ka'idar da ta tanadi yawan wa'adin shekaru biyar-biyar da shugaba zai yi a kan mulki.

A ranar jumma'a kotu mafi girma ta Jamhuriyar Nijar ta yanke hukumcin cewa gudanar da irin wannan kuri'ar raba-gardama haramun ne, amma shugaba Tandja yace zai ci gaba da wannan shiri nasa na yin tazarce. Haka kuma, shugaban na Nijar ya rushe majalisar dokoki, yana mai fadin cewa ana bukatar yin hakan don tabbatar da kwanciyar hankali a kasar mai arzijkin karfen Uranium.

A bayan wadanda suka yi zanga-zanga jiya a Dosso ma, wasu gungun jam'iyyun siyasa da kungiyoyin kwadago sun hada karfi wuri guda domin su yaki kokarin shugaban da masu taya shi buga gangar tazarce. Da alamun ita kanta jam'iyyar MNSD ta shugaba Tandja kanta yana rabe game da wannan batun, inda wasu 'ya'yan MNSD suke goyon bayan tsohon firayim minista Hama Amadou, mutumin da aka jima ana ganin zai yi takarar shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG