Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Ci Gaba Da Kokarinsa Na Yin Tazarce, Tandja Ya Rushe Kotun Tsarin Mulkin Jamhuriyar Nijar


Litinin din nan shugaba Mamadou Tandja na Jamhuriyar Nijar ya rushe Kotun Tsarin Mulkin Kasar, a bayan da ta yanke hukumcin cewa shirinsa na gudanar da zaben raba-gardama a kan ya zarce da mulkin kasar ya saba da dokar kasa.

Tun fari, shugaba Tandja ya maye gurbin ministoci akalla bakwai daga cikin takwas da suka yi murabus a makon da ya shige domin nuna rashin yardarsu da kokarinsa na sauya tsarin mulki da nufin ya nemi wa'adi na uku a kan mulki. Wa'adi na biyu, kuma na karshe bisa tanadin tsarin mulkin kasar, zai kare a watan Disamba.

A ranar lahadi gwamnatin Nijar ta ce lallai zata ci gaba ta gudanar da wannan kuri'ar raba-gardama, duk da cewa Kotun Tsarin Mulki ta sake yanke hukumcin cewa yin hakan haramun ne.

Shugaba Tandja ya kara haddasa tankiyar siyasa a Jamhuriyar Nijar a bayan da ya sanar a ranar jumma'a cewa daga yanzu, dukkan ikon mulkin kasa ya koma hannunsa, watau zai ringa mulki ta hanyar fito da takardar umurnin shugaban kasa.

'Yan hamayya sun bayyana wannan mataki na shugaban a matsayin juyin mulki, sun kuma yi kira ga dakarun tsaron kasar da su ki bin duk wani umurnin da shugaba Tandja zai ba su.

Dubun dubatan mutane sun yi maci a Yamai, babban birnin kasar a cikin watan nan domin su nuna kyamar wannan shiri na Mamadou Tandja na dawwamar da kansa a kan kujerar shugabancin Jamhuriyar Nijar.

Haka kuma, shirin nasa ya janyo tofin Allah tsine daga shugabannin kwadago, da hukumomin kasashen Afirka da kuma gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG