Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Man Shell Zai Biya Diyyar Dala Miliyan Goma Sha Biyar Ga Wasu 'Yan Nijeriya


Kamfanin man fetur na Shell ya yarda zai biya dala miliyan 15 da dubu dari biyar ga wadanda suka kai kararsa bisa zargin hannu a keta hakkin bil Adama a Nijeriya, domin su janye wannan karar.

Wannan yarjejeniyar biyan kudin da aka cimma jiya litinin a New York ita ta kawo karshen shari’ar da aka shafe shekaru fiye da gom ana gwabzawa a tsakanin kamfanin Shell da ‘yan’uwan masu zanga-zangar da tsohuwar gwamnatin mulkin soja ta Nijeriya ta yankewa hukumcin kisa a 1995.

Mutanen sun hada da marubucin wakoki Ken Saro-Wiwa, wanda ya jagoranci zanga-zangar rashin amincewa da zaman kamfanin Shell a yankin Niger Delta. Masu zanga-zangar sun ce kamfanin Shell ya gurbata yanayin yankin ya kuma keta hakkin ‘yan kabilar Ogoni.

Haka kuma sun zargi kamfanin da laifin hada baki da gwamnati wajen hukumta wadanda suka soki lamirin kamfanin. Kamfanin Shell dai ya ce shi bai aikata wani laifi ba, amma yace ya yarda mutanen sun sha wahala.

XS
SM
MD
LG