Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madaukakiyar Kotun Nijar Ta Soke Umurnin Da Shugaba Tandja Ya Bayar Na Shirya Zaben Raba-Gardama A Watan Agusta


Madaukakiyar kotun Jamhuriyar Nijar ta yanke hukumcin cewa shirin shugaba Mamadou Tandja na gudanar da kuri'ar raba-gardama domin kara tsawon wa'adinsa a kan mulki ya saba ma doka, saboda haka haramun ne.

Jiya jumma'a kotun tsarin mulki ta Jamhuriyar Nijar ta ce ta soke umurnin da shugaba Tandja ya bayar ranar 5 ga watan Yuni a kan a gudanar da kuri'ar raba-gardamar a cikin watan Agusta.

Kotun ta ce umurnin da shugaban ya bayar ya saba ma tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar. Tsarin mulkin ya kayyade cewa shugaban kasa zai iya yin wa'adi biyu ne kawai na shekaru biyar-biyar a jere kan mulki.

Shugaba Tandja ya ce yana son karin lokaci a kan kujerar shugaban kasar domin ya kashe wutar tawayen da Abzinawa suke yi, da fadada ayyukan samar da kayan bukatu da kuma ba da karin iko ga kujerar shugaban kasa.

Wannan shiri nasa ya hassala 'yan hamayyar siyasa da shugabannin kwadago na Jamhuriyar Nijar. Haka kuma, hukumomin kasashen Afirka da kuma gwamnatin Amurka sun fito da kakkausar harshe su na sukar lamirin wannan shirin yin Tazarce.

Wa'adin shugaba Tandja a kan mulki zai kare a watan Disamba, amma ya sha nanata cewa ya kamata a canja wannan.

A can baya, kotun tsarin mulkin ta ayyana cewa shirin Tazarcen na shugaba Tandja ya keta doka. A bayan wannan ne sai shugaban ya rushe majalisar dokoki. Sai dai kuma hukumcin da Kotun Tsarin Mulkin ta yanke a jiya jumma'a, hukumci ne da tsarin mulkin kasar ya bukaci cewa tilas a yi aiki da shi.

XS
SM
MD
LG