Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar-Bakin-Wake Ya Kai Farmaki Kan Hukumar Leken Asirin Pakistan


Jami'an tsaron Pakistan sun ce wani dan harin bam na kunar-bakin-wake a cikin mota ya kai farmaki a kan ginin babbar hukumar leken asirin Pakistan, safiyar Jumma'a a birnin Peshawar dake arewa maso yammacin kasar, ya kashe mutane akalla bakwai. Wasu mutanen su talatin da biyar sun ji rauni a wannan harin.

Bam din da ya tashi ya lalata wani gini na hukumar leken asirin Pakistan da ake kira "Inter-Services Intelligence Agency" wadda ta ke kula da akasarin kyamfe na murkushe ta'addanci da ake gudanarwa a yankunan da suek bakin iyaka da Afghanistan.

Wani wakilin Muryar Amurka a birnin Islamabad ya ce bam din da ya tashi yana da karfin da har an ji kararsa a wurare masu nisan kilomita 20 daga wurin.

A wani lamarin, wani dan harin kunar-bakin-waken dabam a cikin mota ya kai farmaki kan wani caji ofis na 'yan sanda a kusa da garin Bannu na arewa maso yammacin kasar, ya raunata mutane akalla 10.

'Yan tsagera sun kaddamar da hare-hare masu yawa tun lokacin da gwamnati ta kaddamar da farmakin murkushe 'yan Taliban a yankin Waziristan ta Kudu a tsakiyar watan Oktoba.

XS
SM
MD
LG