Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Rajin 'Yancin Yammacin Sahara Ta Ki Karbar Takardar Zama 'Yar Kasa Da Spain Ta Ba Ta


Wata sananniyar 'yar rajin 'yancin Yammacin Sahara wadda take yajin cin abinci na tsawon makonni biyu a wani filin jirgin saman kasar Spain, ta ki yarda da tayin da Spain ta yi mata na ba ta takardar zama 'yar kasar domin a taimaka mata ta koma kasarta ta haihuwa, Morocco.

Lauyar Aminatou Haidar a kasar Spain, Ines Miranda, ta ce Aminatou, mai shekaru 42 da haihuwa, ta ki yarda da wannan tayin lokacin da ta gana jiya lahadi da wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Spain a filin jirgin saman Lanzarote dake tsibiran Canary.

Magoya baya sun ce lafiyar Aminatou Haidar ta tabarbare sosai, tun lokacin da ta fara yajin cin abinci a filin jirgin a bayan da Morocco ta kwace mata fasfo ta kuma kore ta daga cikin yankin na Yammacin Sahara da ake rikici kai a wannan watan.

Hukumomin Morocco sun ce sun kama Haidar a ranar 13 ga watan Nuwamba a bayan da suka ce ta ki yarda ta rubuta sunan kasarta a inda aka bukaci a takardar kwastam da ake cikawa lokacin shiga kasar a lokacin da ta koma daga Amurka inda aka ba ta wata kyauta ta kare hakkin bil Adama.

Haidar tana son komawa gida, amma lauyarta ta ce ba ta sha'awar karbar takardar zamowa 'yar kasar Spain domin ba ta son komawa kasarta ta zauna a matsayin bakuwa 'yar kasar waje.

Haidar ta fusata da kasar Spain, wadda ta zarga da laifin goyon bayan Morocco ta hanyar karbarta a bayan da aka kore ta daga yankin Yammacin Sahara. Morocco ta kamfaci akasarin yankin ta maida nata a bayan da Spaniyawa suka janye a shekarar 1975.

XS
SM
MD
LG