Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Tana Cimma Gagarumar Tazara Wajen Kawar Da Cutar Zazzabin Cizon Sauro Ko Maleriya...


Wakili na Musamman na Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yaki da cutar maleriya ko zazzabin cizon sauro a duniya, Ray Chambers, ya bayyana cikakkiyar gamsuwa da irin tazarar da Nijeriya ta cimma cikin shekara guda da ta shige wajen yaki da wannan cuta a kasar.

Mr. Chambers ya ce wannan cuta ta maleriya, ta fi yin illa ga Nijeriya fiye da kowace kasa a doron duniya, domin kimanin kashi 25 daga cikin 100 na wadanda cutar ta ke kashewa a kowace shekara 'yan Nijeriya ne.

Amma jami'in na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana yadda a cikin shekara daya tak, Nijeriya ta cimma matsayin da zata iya tabbatar da gurin babban sakataren Majalisar, Ban Ki-moon, na cewa dukkan 'yan kasar za su samu kayan rigakafi ko na warkar da cutar maleriya nan da karshen shekarar 2010. Ya ce, "irin hazikancin da gwamnatin Nijeriya ta nuna wajen tinkarar cutar maleriya gadan-gadan, wani misali ne na cewa a duk fadin kasashen bakar fata na Afirka, ana iya cimma wannan guri na babban sakataren."

Har ila yau, Chambers ya yaba da ganin cewa yanzu Nijeriya ta kai kanta matsayin da zata iya samun dukkan kudaden da ta ke bukata na saye da raba gidajen sauro har miliyan 70, watau adadin da ake bukata domin tabbatar da cewa kowane dan Nijeriya yana iya kare kansa. Tuni har an samar da kudaden gidajen sauro miliyan 60 daga cikin wannan adadin, tare da tallafin Bankin Duniya, da Asusun yaki da Cutar SIDA, Tarin Fuka da Maleriya a Duniya da kuma wasu cibiyoyin.

Jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa, "Duk wata kasar da ta ke ganin wannan batu na yaki da cutar maleriya babban kalubale ne, to tana iya duba Nijeriya ta ga cewar ana iya samun ci gaba cikin gaggawa a wannan kokari."

Koda yake ana iya rigakafi tare da warkar da cutar maleriya, mutane masu yawa su na mutuwa a sanadinta a saboda babu wadatar kayayyakin rigakafin da kuma magunguna masu nagarta na yakar cutar a hannun mutanen da suka fi bukatarsu, watau talakawa.

'Yan Nijeriya su miliyan 75 ne, watau kimanin rabin al'ummar kasar, suke kamuwa da cutar maleriya mai shiga ta jinin mutum akalla sau daya a kowace shekara, yayin da yara 'yan kasa da shekara 5 da haihuwa su kimanin miliyan 24 a Nijeriya suke kamuwa da wannan cuta wasu har sau hudu a cikin shekara guda.

A fadin duniya dai, mutane miliyan 350 zuwa miliyan 500 ne suke kamuwa da cutar kowace shekara. A kowace rana, maleriya tana kashe yara kanana su dubu 3. A nahiyar Afirka, inda kashi 90 cikin 100 na dukkan mace-macen yara daga zazzabin cizon sauro ke faruwa, cutar ita ce ta fi kashe yara a nahiyar.

XS
SM
MD
LG