Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Bukaci Amurka Ta Cire ta Daga Jerin Kasashen Da Za A Ringa Yi Wa Binciken Kwakwaf


Nijeriya ta bukaci Amurka da ta cire ta daga cikin jerin kasashen da za a binciki fasinjojinsu kwakwaf a duk lokacin da suka nemi zuwa Amurka.

Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ojo Maduekwe, ya fadawa 'yan jarida cewa ya gabatar da wannan bukatar talatar nan a lokacin da ya gana da jakadiyar Amurka a Nijeriya, Robin Sanders, a Abuja, babban birnin kasar.

Amurka ta kara tsananin binciken da za a ringa yi ma fasinjoji daga kasashe 14 ciki har da Nijeriya, a ranar lahadi, kwanaki tara a bayan da wani matashi dan Nijeriya yayi kokarin tarwatsa wani jirgin saman dake kokarin sauka a birnin Detroit a Amurka.

A lokacin da ta ke magana jiya litinin kan wannan batun, ministar yada labarai ta Nijeriya ta ce ba a yi adalci ba wajen sanya Nijeriya a cikin wannan jerin. Dora Akunyili ta ce wannan tamkar danne hakkin mutane miliyan 150 ne a dalilin halayyan mutum daya tak.

Jami'an gwamnatin Nijeriya sun sha nanata cewar dukkan alamu sun nuna cewa a wata kasar waje ce ba a Nijeriya ba shi wanda ake tuhuma, Umar Faruk Abdulmutallab, ya koyi tsagerancinsa.

An yi imanin cewa 'yan al-Qa'ida a kasar Yemen ne suka horas da shi, suka kuma ba shi bam din. Kungiyar al-Qa'ida ta Yankin Arabiya ta dauki alhakin yunkurin harin na bam wanda ya ci tura.

XS
SM
MD
LG