Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Zartaswar Nijeriya Zata Tura Tawaga Don Ganin Shugaba 'Yar'aduwa


Majalisar zartaswar Nijeriya zata tura tawagar mutane 6 domin bin sawun lafiyar shugaban kasar dake kwance yana jinya.

Yau watanni uku ke nan ba a ga shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa ba, tun lokacin da aka kai shi jinyar wani irin ciwon zuciya a kasar Sa'udiyya. Tun lokacin, sau daya tak aka ji wata maganarsa a cikin wata gajeruwar hirar da ya yi ta rediyo.

Ministar yada labarai da sadarwa ta Nijeriya, Dora Akunyili, ta fada yau laraba cewa tawagar majalisar ministocin tana da niyyar ziyartar shugaban tare da ganawa da iyalansa.

'Yan raji da karin jami'an gwamnati su na bayyana damuwar cewa a yanzu shugaba 'Yar'aduwa ya shiga halin da ba zai iya ci gaba da yin mulkin kasar ba.

Tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa ana iya cire shugaban daga kan kujerarsa idan har kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar ministoci suka jefa kuri'ar cire shi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wata tawaga daga Nijeriya ta ke yin tattaki domin binciko gaskiyar lafiyar shugaba 'Yar'aduwa ba.

Jaridun Nijeriya sun buga rahotannin cewa a makon da ya shige wata tawagar majalisar dokokin kasar mai wakilai biyar ta komo bayan da ta shafe kwana da kwanaki tana neman ganin shugaban.

Rahotannin sun ce wakilan sun gana da uwargidan shgaban, Hajiya Turai, amma ba su ga shugaban ba, ba su kuma samu damar magana da shi ko ta waya ba. A ranar asabar suka koma Nijeriya.

XS
SM
MD
LG