Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

kwamandan Rundunar Sojojin Amurka a Afirka Ya Kare Shawarar Barin Hedkwatar Rundunarsa A Jamus


Kwamandan rundunar sojojin Amurka a Afirka ya kare shawarar da aka yanke ta barin hedkwatarsa a kasar Jamus, yana mai fadin cewa duk wani yunkurin maida hedkwatar cikin Afirka zai haddasa matsaloli ne maimakon warware su.

Janar William Ward ya fada lokacin wani zaman sauraron shaida a majalisar dattijan Amurka cewa hedkwatar Rundunar Sojojin Amurka a Afirka zata ci gaba da zama a Jamus na tsawon shekaru masu zuwa. Yace dage hedkwatar da maida ta nahiyar Afirka zasu haddasa rashin fahimta da wasu abubuwan da zasu iya gurgunta ayyukan wannan runduna.

Ina kiyasin cewa duk wani kokarin da za a yi na kafa hedkwatar sojojin Amurka kamar ta wannan runduna a nahiyar Afirka zata kawo mana koma-baya ne. Da sanata McCain ya tambaye shi ko ina dalilinsa, sai yace saboda bahaguwar fahimtar da za a yi ma irin wannan matakin da irin yadda makwabta zasu dauki duk kasar da aka kafa hedkwatar cikinta da dai wasu abubuwan da ba za a ji dadinsu ba. Har ila yau, Janar Ward yace inda hedkwatar rundunar yake ba ya da muhimmanci kamar irin ayyukan da sojojinsa ke yi a fadin nahiyar Afirka.

Yace idan har aikinmu shi ne na habaka kuzarin kasashen Afirka, to abu mafi muhimmanci shi ne irin ayyuka da shirye-shiryen da muke gudanarwa yanzu haka a kasashe 38 a nahiyar. Kuma duk wani yunkuri na neman hedkwata a nahiyar, da batutuwan dake tattare da irin wannan abu, zasu dauke hankali ne daga irin ayyukan da wannan runduna ke gudanarwa a yanzu.

A lokacin da aka kafa wannan runduna a shekarar 2008, ta fuskanci adawa daga shugabanni da kasashen Afirka wadanda suka nuna damuwar cewa yin hakan zata sanya manufofin Amurka a nahiyar ta koma ta soja, tare da kawo yiwuwar tsoma hannun sojojin Amurka a rikice-rikicen nahiyar.

XS
SM
MD
LG