Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gungun Kasashe Masu Shiga Tsakani A rikicin Gabas Ta Tsakiya Sun Yi Allah Wadai Da Isra'ila


Amurka,da Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Turai,da kuma Rasha, sun yi Allah wadai da shawarar da Isra’ila ta tsaida na gina sabbin gidajen ‘yan share wuri zauna a gabashin birnin kudus da take yi wa mamaye.

Kasashen masu shiga tsakani a rikicin gabas ta tsakiya,tareda majalisar dinkin Duniya, sun bada sanarwa jumma’a, cewa duk mataki na gaban kai da aka dauka, bazai sami amincewar kasa da kasa ba. Kasashen masu shiga tsakani sunce za su sa ido sosai kan lamura a birnin kudus,kuma za su yi nazari akai a taronsu na gaba ranar 19 ga watan Maris a birnin Moscow.

Tundafarko a yinin jiya jumma’a,sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta yi kakkausar suka ga Friministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan sanarwar da Isra’ila ta bayar ranar talata na gina sabbin gidaje a gabashin birnin kudus,yanki da falasdinawa suke so ya zama fadar kasarsu nan gaba.

Ahalin yanzu kuma,wata babbar kusa a tarayyar Turai,Catherine Ashton,tace tana ji akwai bukatar gaggawa a warware rikicin Isra’ila dayankin Falasdinu. Ta fadi haka ne a dab da shirin tashin ta lahadi, domin fara rangadi a gabas ta tsakiya.

XS
SM
MD
LG