Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nahiyar Afirka ta yi taron dangi don yaki da barkewar cutar Polio


Sama da yara miliyan 85 yan kasa da shekaru 5 ne za a yi masu rigakafin cutar polio a kasashe 19 na yammaci da tsakiyar Afirka a wani gagarimin yinkuri na bai daya na kasashe da zummar tsayar da annobar polio da ta yi shekara guda ta na barna.

Kasashe 9 a Afirka ta Tsakiya das u ka hada da Burkina Faso, Cameroun, Chad, Guinea, Liberia, Mali, Mauritania, Senegal and Sierra Leone su ne ake daukawa a matsayin masu ci gaba da fama da barkewar Polio (watau wadanda bai wuce watanni 6 da aka gano matsalolinsu ba).

Ran 6watan Maris ne za a fara gangamin a wadannan kasashen dad a kuma Nijeriya, da Ghana da Benin, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Gambia da Cape Verde da Guinea Bissau. Su ko Nijar da Togo da Cote d’Ivore su ma za su bi sahu daga baya au saboda zabukan siyasa au saboda wasu gyare-gyare na siyasa.

Sama da yan aikin sa kai da ma’aikatan jinya wajen 400,000 ne za su shiga wannan aikin.

Kungiyar Rotary ta duniya ce ta dau nauyin wannan gagarimin aiki mai sarkakkiya inda ta samar da dalar Amurka miliyan $30. Da ma dai kungiyar ta Rotary na daya daga cikin masu taimakawa don kawar da polio a duniya.

Daraktan Yankin Afirka na Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), Dr Luis Gomes Sambo, y ace wannan hadaddiyar gangami na tabbatar da aniyar Afirka ta kau da polio daga gare ta. “Tun daga kan kwaloluwa zuwa kan kananan shuwagabanni a kowace kasa” in ji shi , “dukkannin mu alhakin kula da yara a Afirka na wuyarmu---mu yi wa kowane yaro rigakafi mu kuma mu yi nasarar yi a wurare da yawa.”


XS
SM
MD
LG