Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Samu Gagarumar Nasara A Majalisar Wakilan Tarayya


Shugaba Barack Obama Ya Samu Gagarumar Nasara A Majalisar Wakilan Tarayya

<!-- IMAGE -->

Majalisar wakilan tarayya ta nan Amurka ta zartas da gagarumin shirin yin garambawul ga tsarin kiwon lafiya, inda 'yan jam’iyyar Democrat masu rinjaye a cikin majalisar suka mikawa shugaba Barack Obama nasara a wannan fagen da ya maida mafi muhimmanci a batutuwan cikin gida da zai takala.

‘Yan Democrat 219 suka goyi bayan garambawul din. Dukkan ‘yan jam’iyyar Republican da kuma wasu ‘yan Democrat su 34 sun jefa kuri’ar rashin yarda da tsarin. Da ma dai kuri’u 216 ake nema don amincewa ad shirin.

Mr. Obama ya yaba da jefa wannan kuri’a da aka yi. A lokacin da yake jawabi daga bisani a fadarsa ta White House, shugaba Obama yace, "mun kawar da irin tasirin da wasu ‘yan tsiraru masu kare muradun kansu keyi, muka ki mika wuya ga rashin yarda ko tababa ko kuma dai fargabar abinda ke tafe. Mun tabbatar da cewa mu al’umma ce dake iya cimma wani gagarumin abu."

Shugaban ya ci gaba da cewa, wannan kudurin ya amsa addu’o’in wadanda ba su da inshorar kiwon lafiya a Amurka.>

Kafin a fara jefa kuri’ar kuwa, sai da kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi, ta tashi ta roki abokanta ‘yan majalisa da su yi zurfin tunani su amince da wannan kudurin tana mai fadin cewa manufofin tattalin arzikin shugaba Obama sun dogara kan wannan kudurin, inda ta ke cewa "mataki mafi nagarta da zamu iya dauka domin tallafawa kasafin kudi na iyalai a cikin gidajensu da kuma na gwamnatin tarayya shi en mu zartas da kudurin garambawul ga tsarin kiwon lafiya."

An tsara wannan kudurin doka da nufin samar da inshorar kiwon lafiya ga Amurkawa miliyan 32 wadanda ba su da shi a yanzu haka.

'Yan Republican masu sukar lamirin matakin sun ce zai kara tsadar ayyukan kiwon lafiya zai kuma kara tsoma hannun gwamnati a harkokin lafiyar jama’a. Har ma shugaban ‘yan jam’iyyar Republican marasa rinjaye a majalisar wakilai, John Boehner, yayi gargadi yana cewa, "mun ki yarda mu saurari Amurkawa, haka kuma mun ki yarda mu yi aiki da muradun wadanda suka zabe mu."

Shugaba Obama dai yace wannan kudurin dokar da aka zartas a majalisar wakilan ba wai zata magance dukkan matsalolin kiwon lafiya a Amurka ba ne, amma kuma zata gusa da kasar a kan turba ta kwarai. Ana saran shugaba Obama zai rattaba hannu kan wannan kudurin da majalisar ta zartas nan da ‘yan kwanaki.

XS
SM
MD
LG