Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da zarar mutun ko yara sun fara jin ciwon kai, a hamzarta zuwa asibiti don a ga likita cikin gaggawa.


Da zarar mutun ko yara sun fara jin ciwon kai, a hamzarta zuwa asibiti don a ga likita cikin gaggawa.

A bana an samu bullar cutar sankarau a akasarin jihohin arewacin Nigeria. Jihohin da lamarin yafi ta'azzara sune Jigawa, Bauchi, Neja, Kwara da Gombe.

A jihohin Bauchi da Gombe ka dai, mutane 35 suka mutun sanadiyar kamuwa da cutar, yayinda was kusan 70 suke asibiti ana kula dasu.

Babban abinda ke haddasa ciwon sankarau, sune cunkoson mutane da yawa a cikin daki guda mara taga wato wundo. Galibi wadanda suka kamu, suna fara wa ne da ciwon kai mai tsanani, zazzabi kan biyo-baya kafin a ga wuyan wanda ya kamu ya fara sandarewa. Adai dai wannan lokacin ne galibi akan ruga asibiti dan neman magani.

Rigakafin Cutar Sankarau: Sun hada da kwanciya a daki wanda yake da tagogi da kofa bude har zuwa tsawon dare kafin a kulle kofa. Ana kuma son mutane su dai na cunkusuwa a daki guda lokacin zafi.

Da zarar mutun ko yara sun fara jin ciwon kai, a hamzarta zuwa asibiti don a ga likita cikin gaggawa.

A na son mutane su rika zuwa manyan asibitoci a birane idan lokacin zafi ya karato, ko kuma an fara zafi don samun maganin rigakafin ciwon sankarau. A kwai kwayoyi biyu da ake bayar wa na rigakafi.

Jama'a sai ayi hattara.

XS
SM
MD
LG