Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

  Hukumar Taimaka wa Kasashe na Amurka USAID.


  Hukumar Taimaka wa Kasashe na Amurka USAID.

<!-- IMAGE -->

Hukumar Taimaka wa Kasashe na Amurka (USAID) ta himmantu ga inganta lafiyar mata da yan mata ta wajen tallaba wa shirye-shirye na kasa-da-kasa na bunkasa ilimin mata; da hakkokin mata kamar yadda doka ta tanada da kuma shigarsu harkokin siyasa da na tattalin arziki; da kuma ingantacciyar hanyar samun bayanai da kuma kulawa na kiwon lafiya da kuma hana safarar bil'adama, wadanda kowannensu ke taimakawa wajen daukaka matsayin mata.

Taken Ranar tunawa da mata na 2010 shi ne, Equel Rights, Equel Opportunity, Progress for All. Ma'ana: bai wa kowa dama daidai da kowa; bai wa kowa sukuni daidai da kowa; bai wa kowa damar ci gaba.

Cibiyar USAID ta bunkasa kiwon lafiya a duniya tun da dadewa ta lura cewa mata ne su ka fi fama da rashin wadatattun harkokin kula lafiya. Akan bai wa mata makamai irir-irir na aikin kiwon lafiya, da suka hada da tsarin iyali na yaddar rai, kula uwa da jariri da kuma kula da masu ciwon HIV-AIDS da hana yaduwar cutar.

Kuma bayan da Amurka ta bullo da shirinta na Aikin Inganta kiwon lafiya a duniya(GHI) a takaice, mun himmantu a wadannan aikace-aikacen a kokarinmu na ganin mun cimma wannan burin a GHI: Wanda ya hada da Inganta harkokin lafiya a tsakanin mata da yan mata ta wajen tallaba tsarin kawo canji sannu a hankali don kawar da duk wani shamaki a batun samar da ingantaccen yanayin koshin lafiya ga mata; wanda ya hada da sanya maza da yan maza a batutuwan daina nuna bambanci ga mata da kuma kara horar da jami'an kiwon lafiya game da batutuwan daidaito tsakanin jinsi, da tabbatar da cewa mata da yan mata su na shiga ana damawa da su a lokutan yanke shawara; da kuma shigar da kungiyoyi masu zaman kansu da ke kasashen da ke cikin wannan aikin don a tabbatar da daidaiton jinsi a bangaren kiwon lafiya.

XS
SM
MD
LG