Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin Alluran Rigakafi ga yara yan kasa da Shekara Biyar.


Muhimmancin Alluran Rigakafi ga yara yan kasa da Shekara Biyar.

<!-- IMAGE -->

Alluran rigakfi suna da muhimmanci ga rayuwar yara kanana domin alokacin basu da wadatar garkuwar jiki mai kare biladama daga kamu wa da cututtuka masmman daga ranar haihuwa har zuwa shekara biyar a duniya.

Alluran rigakafi sun kasu iri-iri. Akwai BCG da BPT, HPV, CSM, Yellow Fever da kuma Measles.

Su wadan nan alluran suna kare yara daga kamu wa da cutuka shidda masu saurin hallaka yara kamar su tarin fuka da tarin shika, da ciwon hanta, bakon-dauro, ciwon shawara da sarke hakora. Haka nan kuma an digawa jarirai da ‘yan kasa da shekara biyar ruwan allurar rigakafin cutar shan-Inna wato Polio da kuma CSM ta sankarau a lokacin zafi.

Ana fara allurar rigakafi da zarar an haihu jim kadan bayan an tsaftace jariri. Shi ya sa haihuwa a asibiti take da muhimmanci domin duk yaron da ba a haifa a asibiti ba, baya samun ita wannan allura da ake ce mata BCG ta tarin fuka kamar yadda bayani ya gabata. Iyayen da kansu yaw aye, suna rugawa asibiti cikin hamzari bayan an tsaftace jariri don ayi mai rigakafin.

A asibiti ake yin wadan nan alluran kuma su ma’aikatan asibiti, sune zasu fada wa uwargida ranar da zata sake zuwa dan ci gaba da alluran domin ba a lokaci daya ake yin su ba. Yana kai wa tsawon wata tara kafin a gama. A hakikanin gaskiya tsakanin ta farko da ta biyu yana kai wa mako 4 zuwa 6, to amma ya dangata ne daga bayanan ma’aikatan jiyya na asibiti..

Duk yaran da iyayensu ke kai su asibiti don karbar alluran rigakafin, za ka gansu cikin koshin lafiya da kumari, ga kuma kaifin basira da yin girma cikin sauri.

Asaboda haka, ya kamata iyaye su kara himmatuwa zuwa asibiti don yiwa ‘ya’yansu alluran rigakafin.

XS
SM
MD
LG