Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliyawa 'Yan Fashi Sun Nausa Tsakiyar Teku Don Fashin Jiragen Ruwa


Somaliyawa 'Yan Fashi Sun Nausa Tsakiyar Teku Don Fashin Jiragen Ruwa

<!-- IMAGE -->

Rundunar mayakan ruwan Tarayyar Turai ta ce Somaliyawa 'yan fashi cikin teku, sun nausa can tsakiyar tekun Indiya, inda ba su saba kaiwa ba, suka yi fashin wasu jiragen kamun kifi guda uku na kasar Thailand da ma'aikatansu su 77.

Kakakin rundunar ta Tarayyar Turai, Kwamanda John Harbour, ya fada a yau talata cewa Somaliyawan sun yi fashin wadannan jirage a wuri mai tazarar kilomita dubu biyu daga gabar kasar Somaliya. Kakakin yace wannan shi ne karon farko da aka yi fashin jirage a wuri mai nisa daga gaba kamar haka. Asali ma dai in ji Kwamanda Harbour, wurin da aka yi fashin jiragen ya fi kusa da gabar kasar Indiya a kan gabar kasar Somaliya.

Sintirin da jiragen ruwan yaki na kasashen Turai da Amurka suke yi a kusa da gabar kasar Somaliya, ya sa yanzu 'yan fashin su na kara nausawa can cikin teku domin far ma jirage.

Hukumomi sun ce da alamun ma'aikatan jiragen kamun kifin na Thailand da aka yi fashi su na nan kalau, kuma a yanzu haka wadannan jirage sun doshi gabar kasar Somaliya.

Somaliyawa 'yan fashi sun kama jiragen ruwa fiye da ashirin tun daga farkon watan Maris, kuma a yanzu haka su na rike da ma'aikata fiye da 200 na jiragen su na yin garkuwa da su. A yawancin lokuta ana sake jiragen da ma'aikatansu da zarar an biya 'yan fashin kudin fansa.

XS
SM
MD
LG