Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban China Yayi Alkawarin Tallafawa Afghanistan - 2002-01-24


Kasar China ta ce shugaba Jiang Zemin ya yi alkawarin bada gudumawar karin kudi dala milyan 150, a irin agajin da ake bayarwa domin sake ginin kasar Afhganistan, wadda yaki ya dai-daita. Kamfanin dillancin labaran China, Xinhua, ya ce Mr. Jiang ya yi wannan alkawari ne a lokacin wata tattaunawa yau, shi da shugaban gwamnatin rikon-kwaryar Afganistan Hamid Karzai, wanda a yau din yake kammala wata ziyarar kwana biyu da ya kai kasar China.

Dama dai tuni gwamnatin ta birnin Beijing ta yi alkawarin bada gudummawar dala milyan hudu da dubu dari shida. Malam Karzai, wanda wani lokaci a yau alhamis zai zarce zuwa kasar Tajikistan, ya isa kasar ce ta China, bayan da a farkon wannan makon aka yi masa alkawarin gudummawar dala milyan dubu hudu, da milyan dari biyar, yayin wani taro da hukumomi, gami da kasashe masu bada agaji suka yi a birnin Tokyo, kasar Japan.

XS
SM
MD
LG