Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Gwamnatin Shugaba Bush Suna Muhawara Mai Zafi Kan Fursunonin Afghanistan - 2002-01-28


Jami’an gwamnatin Bush na tafka mahawarar yadda zasu kira fursunonin mayakan al-Qa’ida dana Taleban da yaki ya ci. A wani lokaci a yau majalisar tsaron kasa ta Amurka zata yi muhawara kan wannan batu.

A jiya lahadi, sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya bayyana wadannan fursunonin a matsayi masu hatsarin gaske, makisa da duniya ba zata dauke su a matsayin fursunonin yaki ba, kamar yadda aka saba.

Amma labari na fadin cewa ma’aikatar harkokin kasashen wajen Amurika na bukatar abi ka’idodin yarjejeniyoyin Geneva na fursunonin yakin, yadda sojojin Amurika da yaki yaci, za’a daukesu tamkar fursunonin yakin ba tare da wata nifaka ko tsangwama ba.

Karkashin yarjejeniyyar Geneva, fursunonin yaki ba’a matsa masu su bada labarin irin harin da sojojin abokan gaba zasu kai ko suke shirin kaiwa.

XS
SM
MD
LG