Rikicin kabilanci ya sake barkewa a birnin Lagos, babbar cibiyar harkokin kasuwanci ta Nijeriya, bayan arangamar da aka yi a karshen mako, inda aka kashe fiye da mutane 20.
Shaidun gani da idanu, sun ce an samu karin gawarwaki akan titunan unguwar Mushin, a sakamakon fadan da aka gwabza a daren jiya. Fadan, ya kuma yi sanadiyyar yin kaurar wasu mutanen masu yawa daga gidajensu.
Nan take dai, ba a san ko mutane nawa ne suka mutu, ko kuma jikkata ba, a sakamakon sabon rikicin.
A shekaranjiya asabat ne, aka kacame bata-kashi a tsakanin Hausawa, ‘yan arewacin Nijeriya, da kuma Yarbawa na kudancin kasar. Ba a san tartibin abinda ya haddasa wannan badakala ba a tsakanin kabilun biyu.
Wannan sabon rikici dai, ya kunno kai ne, a daidai wannan lokaci da kasar ta Nijeriya take juyayin mutuwar akalla mutane dubu daya, a sanadiyyar fashewar wasu albarusai cikin makon jiya, a wani runbun ajiye makamai dake birnin na Lagos.