Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Hallaka Falasdinawa Biyar - 2002-02-04


An kashe wasu wakilan bangaren Falasdinawa mai ra’ayin canji ko-da-gora su biyar yau litinin, bayan tashin wani bam a cikin karamar motarsu a Zirin nan na Gaza.

Jami’an Falasdinawa sun yi amanna cewa, wani makami mai linzami da wani jirgin Isra'ila mai saukar angulu ya harba, shi ne ya yi raga-raga da wannan mota. Amma rundunar sojin Isra'ila ta ce, ita ba ta da wata masaniya gameda afkuwar wannan lamari.

Mutanen biyar da aka kashe dai, wakilai ne na kungiyar hankoron tabbatar da demokradiyya da kwatar ‘yancin Falasdinu.

XS
SM
MD
LG