Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Suna Dafawa 'Yan Sanda A Lagos - 2002-02-04


An aika da sojojin Najeriya suje su hade da ’yan sanda domin shawo kan tarzomar kabilanci tsakanin Hausawa da Yarbawa da yanzu akayi kwanaki uku na yi a can Lagos, babbar cibiyar kasuwancin Najeriya.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce sama da mutum hamsin da biyar sun hallaka, yayin da wasu mutum kusan dari da hamsin da biyar suka ji rauni.

Daruruwan mutane sun fice sun gudu daga gidajensu, musabbabin wannan takaddamar tsakanin Hausawa da Yarbawa, da aka yi ta tabkawa da bindigogi, takkubba, adduna tare da wasu makamai, ana kuma bi ana sa wuta a gidajen mutane, wadanda basu san hawa ba, ba su san sauka ba.

Gwamna Tinubu na Lagos, anji ya ambaci cewa ya umurci ma’aikatan tsaro su hukunta duk wani mai tada zaune tsaye, ba sani ba sabo, yayin da shedun gani da ido na fadin cewa fadan da aka gwabza cikin dare ya bar gawarwakin mutane birjik a kan titunan gundumar Mushin, a birnin na Lagos.

Har yanzu an kasa fahimtar salsalar wannan tarzoma data barke shekaranjiya tsakanin Hausawa da Yarbawa, amma labari na fadin cewa al’amarin duk aikin ’yan takifene zauna gari banza.

Wannan tarzomar ita ce ta baya bayan nan a Najeriya, wadda har yaznu bata gama ji da hasarar da akayi a makon jiya ba, sanadiyar fashewar alburushe da nakiyoyi a runbun ajiye makaman yaki dake Ikeja a Lagos din.

XS
SM
MD
LG