Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Tsaron Nijeriya Sun Maido Da Zaman Lafiya a Titunan Ikko - 2002-02-06


Jami’an tsaron Nijeriya cikin damara sosai sun maido da zaman lafiya a unguwanin birnin Lagos, abinda ya kawo karshen kwanakin da aka yi ana rikicin kabilanci, har ma aka hallaka mutane akalla dari daya.

Dubban mutane sun arce daga gidajensu tun ranar asabar data shige a lokacin da aka fara arangama tsakanin Hausawa da Yarbawa.

Kungiyoyin biyu sun fafata da bindigogi da adduna da wasu makaman, sannan kuma suka bankawa wasu gine gine wuta.

Har yanzu ba’a tantance da abinda ya haddasa wannan tarzoma ba.

Jami’an kungiyar agaji ta Red Cross sunce an raunata daruruwan mutane, kuma mutum dubu uku ne suka nemi mafaka a sansanin wucin gadi da aka kafa.

Sa’annan kuma gashi har yanzu Nijeriya na kokarin murmurewa daga fashe-fashen nakiyoyi a rumbun adana makamai a Lagos, abinda ya hallaka mutane akalla dubu daya, yayin da wasu dubban mutanen suka yi hasarar gidajensu.

XS
SM
MD
LG