Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Charles Taylor Ya Kafa Dokar-Ta-Baci a Liberiya - 2002-02-08


Shugaba Charles taylor na Liberiya ya kafa dokar-ta-baci a kasar domin ya samu sukunin yakar ’yan tawaye.

A cikin jawabin da yayi ta rediyo ga al’ummar kasar a yau Jumma’a, shugaba Taylor ya ce halin da ake ciki na bukatar kafa dokar-ta-bacin, yana mai cewa wannan yayi daidai da tanadin tsarin mulkin kasar. Mr. Taylor ya soki takunkumin makaman da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta kafawa Liberiya, matakin da ya ce ya taimaka wajen rura wutar tawayen. MDD ta kafa wannan takunkumin hana sayar da makamai a saboda taimakon da Liberiya take bai wa ’yan tawaye a Saliyo makwabciyarta.

Kungiyar ’yan tawaye mai suna Hadin Kan ‘Yan Liberiya Masu Rajin Sasantawa da Wanzar da Dimokuradiyya, ita ce take yakar gwamnatin Mr. Taylor.

Wannan tawaye yana da cibiya, ya kuma fi karfi a lardin Lofa dake arewacin kasar, amma kuma akwai alamun fadan yana yaduwa. Gwamnatin Liberiya tayi ikirarin cewa ta fatattaki wani harin da ’yan tawaye suka kai a kan garin Klay Junction, kimanin kilomita 40 a arewa da Monrovia, babban birnin Liberiya. Babu wata kafa mai zaman kanta da ta gaskata wannan ikirarin.

Dubban mutane sun guje ma fadace-fadacen da ake yi suka koma yankunan dake kusa da Monrovia, babban birnin kasar. Shi kansa Mr Taylor tsohon madugun ’yan tawaye ne, wanda aka zaba a 1997, a karshen yakin basasar shekaru 7 da yayi kaca kaca da wannan kasa dake Afirka ta yamma.

XS
SM
MD
LG