Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zimbabwe Ta Ce Ko A Jikinta... - 2002-02-19


Gwamnatin Zimbabwe ta fito tana yin ko oho da shawarar da Kungiyar Tarayyar Turai, KTT, ta yanke ta kakabawa gwamnatin kasar takunkumi a saboda korar jagoran ’yan kallon zabe na kungiyar.

Ministan yada labarai, Jonathan Moyo, ya bayyana matakin na KTT a zaman na nuna kiyayya, ya kuma lashi takobin cewa Zimbabwe zata kare ’yanci da diyaucinta.

Magoya bayan gwamnati da dama sun yi zanga-zanga a Harare, babban birnin kasar, domin nuna rashin jin dadin sanya takunkumin. Shaidu sun ce 'yan zanga-zanga sun yi ta jefa duwatsu kan gine-gine, ciki har da na jam'iyyar adawa ta MDC.

A jiya litinin, ministocin harkokin wajen KTT dake yin taro a birnin Brussels suka sanyawa shugaba Robert Mugabe da wasu mukarrabansa su 19 takunkumi, aka haramta musu ziyarar duk wata kasa ta kungiyar tare da garkame dukiyoyi da kadarorinsu a cikin wadannan kasashe.

Har ila yau ministocin harkokin wajen KTT sun yanke shawarar janye dukkan ’yan kallon zabe na kungiyar da aka tura Zimbabwe domin sa idanu kan zaben shugaban kasar da za a yi a ranakun 9 da 10 ga watan gobe na Maris. KTT ta yanke wannan shawara a bayan da gwamnatin Mr. Mugabe ta kori jagoran 'yan kallon dan kasar Sweden, Pierre Schori.

Zimbabwe ta haramta 'yan kallon zabe daga kasashen Sweden, Britaniya, Jamus, Denmark, Finland da Netherlands ko Holland, tana mai zargin cewa sun tsani gwamnatin kasar.

Har ila yau gwamnatin Mr. Mugabe ta haramtawa 'yan jaridar kasar Sweden shiga Zimbabwe domin dauko rahotannin wannan zabe. Har ila yau an ki yarda da wasu 'yan jaridar kasashen Turai da Afirka ta Kudu.

XS
SM
MD
LG