Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Zata Kafa Shamaki Tsakaninta Da Falasdinawa - 2002-02-21


Isra’ila ta ce zata kafa wani shamakin tsaro da zai raba tsakaninta da Falasdinawa.

Firayim ministan Isra’ila, Ariel Sharon, shi ya bayyana wannan cikin wani jawabin da yayi ma ’yan Isra’ila a daidai lokacin da jiragen kai farmaki masu saukar ungulu na Bani Isra’ila suke kai hare-hare a dare na uku a jere kan cibiyoyin falasdinawa a zirin Gaza.

Sabbin hare-haren sun zo a bayan da shugaban Falasdinawa Yasser Arafat ya sake yin rokon da a tsagaita bude wuta a wannan tashin hankali dake kara yin muni.

Sojojin Isra’ila sun kashe karin Falasdinawa guda 8 yau alhamis a Gaza da yankin yammacin kogin Jordan a ci gaba da kai farmakin da suke yi tun bayan da sojojin bani Isra’ila 6 suka sheka barzahu ranar talata a yankin yammacin kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG