Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun 'Yan Adawa Ya Ayyana Kansa Shugaban Kasar Madagascar - 2002-02-22


Madugun ’yan adawan kasar Madagascar, Marc Ravalomanana, ya ayyana kansa a zaman shugaban wannan tsibiri, duk da jan kunnen da gwamnatin kasar da kuma kasashen waje suka yi masa.

Mr. Ravalomanana ya zo na farko, koda yake bai samu fiye da rabin dukkan kuri'un da aka jefa ba, a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Disamba, amma yayi zargin cewa shugaba Didier Ratsiraka, wanda ya jima yana mulkin wannan tsibiri, yayi magudi a zaben. Madugun ’yan adawan ya ce ba zai shiga cikin zagaye na biyu na zaben fitar da gwani da za a yi a karshen wata mai zuwa ba.

A yau Jumma’a, Mr. Ravalomanana ya ayyana kansa shugaban kasa a gaban dubban magoya bayansa, wadanda suka yi gangami a cikin filin wasa na Antananarivo, babban birnin kasar. Su ma shugabannin coci-cocin kasar sun halarci taron.

Tun ma kafin gangamin na yau, gwamnatin Madagascar tayi tur da aniyar Mr. Ravalomanana ta ayyana kansa a zaman shugaba. Gwamnatin Madagascar ta ce a shirye dakarun tsaron kasar suke su kare mulkin doka.

A jiya alhamis, shi ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya bayyana damuwa sosai kan matakan da Mr. Ravalomanana yake dauka, yana mai cewa bai yarda da duk wani yunkurin karbar mulki ta hanyar da ba ta shimfide cikin tsarin mulki ba.

XS
SM
MD
LG