Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karzai Yayi Jawabi Cikin Zauren Majalisar Dokokin Iran - 2002-02-25


Shugaban gwamnatin rikon-kwaryar Afghanistan, Hamid Karzai, ya yi jawabi ga majalisar dokokin kasar Iran a yau litinin, inda ya shedawa 'yan majalisar a birnin Tehran cewa tilas ne kasashen biyu makwabtan juna su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Mr. Karzai ya yabawa Iran saboda irin tallafin data baiwa Afghanistan a lokacin da tsohuwar tarayyar Sobiyat ta mamaye kasar. Ya ce, dangantaka da amincin dake tsakanin kasashen biyu, dangantaka ce mai karfin gaske saboda kasashen biyu suna da al'ada da harshe iri guda.

Gwamnatin Iran da gwamnatin Amurka suna fama da sabani game da yadda gwamnatin ta Iran take gudanar da huldarta da makwabciyar tata daga gabas. Gwamnatin Amurka ta yi zargin cewa Iran tana kokarin wargaza kasar ta Afghanistan, tare da bayar da mafaka ga 'yan Taleban da mayakan Al-Qa'ida da suka arce.

Gwamnatin Iran ta musanta wannan zargi, tana cewa ita tana bayar da cikakken goyon-baya ga gwamnatin Mr. Karzai.

XS
SM
MD
LG