Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Tattauna Shirin Zaman Lafiya A Kwango-Kinshasa - 2002-02-25


A Afirka ta Kudu, an bude taron shawarwarin neman zaman lafiya da nufin kawo karshen yakin basasar da ake gwabzawa a Kwango Kinshasa.

Shugaban Kwango Kinshasa, Joseph Kabila, da kungiyoyin adawa, da wakilan jama'a da kuma bangarorin 'yan tawayen da suka balle daga manyan kungiyoyin tawaye na kasar, suna halartar wannan taro da ake yi a garin 'yan yawon shakatawa mai suna Sun City.

Madugun daya daga cikin manyan kungiyoyin 'yan tawayen Kwango-Kinshasa, Jean Pierre Bemba, yana can Afirka ta Kudu domin halartar wannan taron shawarwari, duk da sanarwar da ya bayar a makon da ya shige cewar ba zai tura tawaga zuwa zauren taron ba. Mr. Bemba, wanda ke shugabancin kungiyar 'yan tawaye ta "Congolese Liberation Movement," ya ce kungiyoyin adawa ba su da wakilci sosai a zauren taron.

Ana sa ran za a shafe kwanaki 45 ana yin tattaunawar da manufarta ita ce shata yadda za a shimfida mulkin dimokuradiyya cikin kwanciyar hankali a wannan kasa da ake kira Zaire a da.

A ranar lahadi, gwamnatin Kwango Kinshasa ta zargi Rwanda da 'yan tawaye kawayenta da laifin karya haddin shirin tsagaita wuta, ta hanyar kai hari kan sojojin gwamnati a yankin kudu maso gabashin kasar.

An fara yakin basasa a Kwango Kinshasa a shekarar 1998, lokacin da 'yan tawaye masu samun goyon bayan Uganda da Rwanda, suka fara tawaye domin kifar da gwamnati a birnin Kinshasa. Angola da Namibiya da Zimbabwe sun tura sojoji domin tallafawa gwamnatin Kwango Kinshasa a wannan rikicin, wanda ya raba kan kasar, ya kuma lankwame rayukan mutane kimanin miliyan biyu.

XS
SM
MD
LG