Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yayi Marhabin Da Shawarar Saudi Arabiya - 2002-02-26


Shugaba Bush yayi marhabin da shirin da kasar Sa'udiyya ta gabatar na wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, yayin da wani babban jami'in Tarayyar Turai yake shirin ziyartar Sa'udiyya domin tattauna wannan shirin.

Shugaba Bush ya buga waya yau talata, domin godewa Yarima Abdullahi mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya saboda wannan shawara da ya gabatar. Wani kakakin fadar White House ya ce Mr. Bush ya yaba da ra'ayoyin da Yarima Abdullahi ya gabatar na kulla cikakkiyar hulda a tsakanin kasashen Larabawa da Isra'ila da zarar an cimma kammalalliyar yarjejeniya ta zaman lafiya.

Babban jami'in hulda da kasashen waje na Tarayyar Turai, Javier Solana, zai katse ziyarar da yake yi a Isra'ila da yankunan Falasdinawa, domin kai wata ziyarar da tun farko ba a tsara ta ba gobe laraba zuwa Sa'udiyya da nufin tattauna wannan shawara. Wani jami'in Tarayyar Turai ya ce Mr. Solana ya yanke shawarar zuwa Jeddah a bayan da ya samu martani na karfafa guiwa game da wannan shawara ta Sa'udiyya daga wajen Falasdinawa da wasu jami'an Isra'ila.

Mr. Solana ya ce firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila yana shirye ya gana da kowane jami'i daga Sa'udiyya domin samun karin bayani game da wannan shawara.

A makon da ya shige Yariman mai jiran gadon Sarautar Sa'udiyya ya gabatar da wata shawara cikin jaridar New York Times, inda yake fadin cewa kasashen larabawa zasu amince da kasar Isra'ila har ma su kulla hulda da ita idan har ta janye daga dukkan yankunan larabawa da ta mamaye a lokacin yakin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967. Yarima Abdullahi ya ce ya dakatar da gabatar da wannan shawara ce a saboda irin matakan da Isra'ila ta dauka cikin 'yan kwanakin nan a yankin Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza.

Ministan tsaron Isra'ila, Benjamin Ben-Eliezer, ya ce shawarar ta Sa'udiyya ta kunshi abubuwa na kwarai, kuma ya kamata a karfafa mata guiwa.

Shi ma ministan harkokin wajen Isra'ila Shimon Peres, ya fada a lokacin tattaunawa a Faransa, cewa wannan shawara ta Sa'udiyya ci gaba ne, yana mai yaba mata. Ya ce a karon farko, Sa'udiyya ta fito a fili tana nuna goyon baya ga shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG