Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Taka Tsantsan Da Amincewar Da Sudan Ta Yi Da Wani Shiri - 2002-03-05


Amurka tana taka-tsantsan wajen yin marhabin da amincewar da gwamnatin Sudan ta yi da wani sabon shirin Amurka na kawo karshen kai hare-haren bam kan fararen hula a kudancin Sudan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Richard Boucher, ya ce gwamnatin Sudan ta bayyana amincewarta da shirin bin diddigin yadda ake aiwatar da shirin, amma kuma ya ce har yanzu 'yan tawayen kungiyar "Sudan People's Liberation Army", ko SPLA, ba su bayyana amincewarsu ba.

Mr. Boucher ya ce hukumomin Amurka suna son bangarorin dake da hannu a yakin basasar Sudan, su fito tsakani da Allah su kuduri aniyar daina kai hare-hare kan fararen hula, su kawo karshen tashin hankalin da ya ki ci, ya ki cinyewa, sannan su amince da girka 'yan kallo na kasashen waje.

Kakakin na Amurka ya ce hukumomi a birnin Khartoum sun yi bayani, tare da neman gafara, kan harin da wani jirgin yaki mai saukar ungulu na gwamnati ya kai a kudancin Sudan a ranar 20 ga watan Fabrairu. Wannan harin da aka kai kan wata cibiyar rarraba agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya kashe mutane 17.

A bayan wannan hari, Amurka ta dakatar da kokarin da take yi na wanzar da zaman lafiya a Sudan, amma Mr. Boucher ya ce a yanzu Amurka tana kokarin farfado da wannan kokari a bayan da hukumomin Sudan suka yi alkawarin daukar kwararan matakan tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.

A jiya litinin, Sudan ta ce ta amince da sabuwar shawarar da Amurka ta gabatar, wadda ta ce ta kunshi cikakken bayanin abinda ake nufi da cibiyoyin fararen hula, tare da yin kiran da a daina yin amfani da su fararen hula a zaman garkuwa. Sudan tana zargin cewa 'yan tawayen Sudan suna yin amfani da fararen hula wajen kange cibiyoyin sojan da aka iya kaiwa hari.

XS
SM
MD
LG