Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Liberiya Suna Tattaunar Yin Sulhu A Abujar Nijeriya - 2002-03-14


An fara hidimar tattaunawa da nufin sasanta al'ummar kasar Liberiya, yau alhamis a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya.

Wakilin Muryar Amurka a yankin Afirka ta Yamma, Luis Ramirez, ya ce wadanda ke wannan tattaunawa sune jami'an gwamnatin Liberiya, da 'yan adawar dake zaune a kasashen ketare. 'Yan tawayen kungiyar nan da ake kira "Liberians United for Reconciliation and Democracy" sun shaidawa Muryar Amurka a yau alhamis cewa wakilansu ba za su halarci wannan taron ba.

'Yan adawar Liberiya dake zaune a kasashen waje suna dari-darin komawa kasar, a saboda fargabar cin zarafi daga jami'an tsaron shugaba Charles Taylor. Wadanda ke halartar wannan taro na Abuja sun hada da wakilan jam'iyyun hamayya, da shugabannin al'umma da kuma baokan adawar siyasa na shugaba Taylor wadanda suke zaune a kasashen waje.

Ana gudanar da wannan tattaunawa a karkashin kulawar kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, Manufar wannan tattaunawa ita ce share fagen taron kolin sasantawa na 'yan Liberiya da za a yi cikin watan Yuli a Monrovia, babban birnin Liberiya.

XS
SM
MD
LG