Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obasanjo Da Mbeki Sun Gana Da Mugabe A Birnin Harare - 2002-03-18


Shugabannin Nijeriya da Afirka ta Kudu sun tattauna a kasar Zimbabwe da shugaba Robert Mugabe da madugun adawa Morgan Tsvangirai, dangane da zaben shugaban kasa na makon jiya da ake yin gardama a kai.

Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya da takwaransa na Afirka ta Kudu, Thabo Mbeki, ba su bada cikakken bayani na sakamakon tattaunawar da suka yi yau litinin ba. An sa ran cewa zasu matsawa Mr. Mugabe lamba kan ya kafa gwamnatin hadin kan kasa. A jiya lahadi aka sake rantsar da shugaba Mugabe a wani sabon wa'adi na shugabanci.

'Yan adawa sun ki yarda da sakamakon zaben, yayin da 'yan kallo da dama na kasashen waje suka yi tur da yadda aka gudanar da wannan zabe.

Nijeriya da Afirka ta Kudu da kuma Australiya, sune wakilan wani kwamitin kungiyar "Commonwealth" wanda aka dorawa alhakin bada shawara kan matakan da za a iya dauka game da kasar Zimbabwe. Gobe talata wannan kwamiti mai wakilai uku zai gana a birnin London.

A can cikin kasar kuma, Kungiyar Masu Noman Kasuwanci ta Zimbabwe, ta ce wasu 'yan banga da ake zaton na jam'iyyar dake mulkin kasar ne, sun bindige suka kashe wani manomi bature yau litinin a kusa da garin Norton, wanda ke yamma da Harare, babban birnin kasar. Wannan manomi shine bature na goma da aka kashe, tun lokacin da 'yan tsagera suka fara mamaye gonakin turawa karfi da yaji shekaru biyu da suka shige.

A cikin jawabinsa na rantsuwa jiya lahadi, Mr. Mugabe ya lashi takobin gaggauta shirinsa na sake fasalin dokokin mallakar filaye da ake cacar-baki kai. Ya ce al'ummar Zimbabwe sun jefa kuri'a cikin 'yanci ba tare da tsangwama ba, domin yin watsi da mulkin mallaka. Ya zargi kasashen yammaci, musamman Ingila wadda tayi musu mulkin mallaka, da laifin goyon bayan Mr. Tsvangirai.

XS
SM
MD
LG