Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce MAi Yiwuwa Cheney Ya Gana Da Arafat - 2002-03-23


Shugaba Bush ya ce mataimakin shugaba Dick Cheney yana iya ganawa da Malam Yasser Arafat, idan har shugaban na Falasdinawa ya kara daukan matakan wanzar da shirin tsagaita wuta a tashin hankalin dake wakana tsakanin 'yan Isra'ila da Falasdinawa.

Mr. Bush ya ce za a iya yin wannan ganawa nan bada jimawa ba idan har wakilin Amurka, Anthony Zinni, ya tabbatar da cewa Malam Arafat ya cika alkawarin da ya dauka na kawo karshen tashe-tashen hankulan watanni 18.

Janar Zinni zai sake ganawa da jami'an tsaron Isra'ila da na Falasdinawa gobe lahadi domin sake kokarin cimma tsagaita wuta a tsakanin sassan. A ranar Jumma'a, janar Zinni ya shaidawa Malam Arafat cewar ba ya yin bakin kokarinsa na kawo karshen wannan fitina.

An bada rahoton sabbin tashe-tashen hankula a yau asabar. Isra'ila ta ce ta bindige ta kashe Falasdinawa biyu wadanda suka kai hari kan wata tashar soja a arewacin Zirin Gaza. An kashe wasu Falasdinawan guda biyu kuma yau asabar da sanyin safiya a kudancin Zirin Gaza, dayansu a lokacin da Isra'ila ta yi luguden wuta kan wani sansanin 'yan gudun hijira a kusa da Rafah.

XS
SM
MD
LG