Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Jinkirta Komawar Tsohon Sarkin Afghanistan Zuwa Kasar - 2002-03-23


Shugaban gwamnatin rikon kwarya na Afghanistan, Hamid Karzai, ya ce an jinkirta komawar tsohon sarkin kasar, Mohammed Zahir Shah, da kwanaki biyu ko uku, kan yadda aka tsaida a da.

Mr. Karzai ya bada wannan sanarwa yau asabar a lokacin taron manema labarai a birnin Kabul, 'yan sa'o'i kadan a bayan da ma'aikatar harkokin wajen Italiya ta ce tsohon sarkin ba zai koma Afghanistan ba sai a wani lokaci a ciki watan Afrilu. Hukumomin Italiya ba su bada wani dalili na wannan jinkiri ba. Amma kuma jami'an Afghanistan a birnin Rum sun ce akwai damuwa game da tsaron lafiyarsa.

Tsohon sarkin mai shekaru 87 da haihuwa yana zaune a birnin Rum tun lokacin da aka tumbuke shi daga kan gadon sarauta shekaru 29 da suka wuce. Da fari an shirya zai koma Afghanistan a ranar talata 26 ga watan nan na Maris.

A halin da ake ciki, dubban yara a Afghanistan sun koma makarantunsu kamar yadda aka shirya. Ga wasu daliban, musamman yara mata, wannan shine karon farko da suka sanya kafa cikin makaranta tun lokacin da 'yan Taleban suka hau kan mulki shekaru biyar da suka shige.

XS
SM
MD
LG