Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Bude Taron Kolin Kasashen Larabawa Ba Tare Da Wasu Muhimman Shugabanni Ba - 2002-03-27


Yau laraba za a bude taron kolin Kungiyar Kasashen Larabawa a birnin Beirut ta kasar Lebanon, duk da cewa shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, da shugaban Misra, Hosni Mubarak, ba zasu samu damar halarta ba.

Jiya talata da maraice jami'an Falasdinawa suka ce Malam Arafat ba zai halarci taron ba, a bayan da Bani Isra'ila ta sanya sabbin ka'idojin kyale shi ya bar yankin Yammacin kogin Jordan, inda sojojin Isra'ila suka yi masa talala tun cikin watan Disamba.

Firayim minista Ariel Sharon ya ce daga cikin sabbin ka'idojin, Isra'ila zata hana Malam Arafat komawa cibiyarsa a yankin Yammacin kogin Jordan, idan har aka kai wa Isra'ila hari a lokacin da yayi wannan tafiya.

Su kuma jami'an Misra sun ce matsalolin cikin gida suka hana Malam Mubarak zuwa wurin taron kolin, amma kuma an ambaci ma'aikatan diflomasiyya suna fadin cewa shugaban na Misra ya fusata ne da cewa Amurka kasa daukar managartan matakan ganin Malam Arafat ya halarci taron kolin.

Jami'an Kungiyar Kasashen Larabawa sun ce duk da haka, taron kolin na kwanaki biyu zai tattauna shirin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya wanda Sa'udiyya ta gabatar, wanda kuma Amurka tayi marhabin da shi. A yanzu, Malam Arafat yana shirin yin jawabi ga masu halartar taron ta tauraron dan Adam.

Shugabannin kasashen Larabawa da dama, da jami'an Majalisar Dinkin Duniya da na Kungiyar Tarayyar Turai suna cikin wadanda zasu halarci wannan taro.

XS
SM
MD
LG