Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharon Da 'Yan Kishin Falasdinu Sun Yi Musanyar Barazana Kan Juna - 2002-04-01


Firayim minista Ariel Sharon ya lashi takobin murkushe Falasdinawa masu zazzafan ra'ayi, yana mai cewa Isra'ila ba za ta sasanta da mutanen da ke son mutuwa domin su kashe fararen hular da ba su san hawa ba balle sauka.

Dakarun Shuhada'u na al-Aqsa sun maida martani jiya lahadi ga Mr. Sharon, suna masu barazanar sako daruruwan 'yan harin kunar-bakin wake domin kai farmaki a biranen Tel Aviv, da al-Qudus, da Haifa da sauran biranen Isra'ila, sai fa idan Isra'ila ta janye daga Ramallah, inda ta killace shugaban Falasdinawa Yasser Arafat a cikin ginin hedkwatarsa da ta lalata a Yankin Yammacin Kogin Jordan.

A halin da ake ciki, sojojin Isra'ila sun sake kwace wani garin na Falasdinawa mai suna Qalqiyah a Yammacin kogin Jordan. Rahotanni sun ce sojojin Isra'ila suna taruwa a kusa da garin Bethlehem.

A daren lahadi, Mr. Sharon ya shaidawa wani gidan telebijin na Amurka cewa a shirye yake yayi tattaki zuwa birnin Washington idan shugaba Bush ay gayyace shi tare da shugabannin Larabawa domin tattauna shirin samar da zaman lafiyar da Sa'udiyya ta gabatar. Shirin yayi kira ga Isra'ila da ta janye daga dukkan yankunan da ta mamaye a yakin Gabas ta Tsakiya na 1967 domin a kulla zaman lafiya da kuma dangantaka tsakaninta da kasashen Larabawa.

Tun da fari a jiya lahadin, hare-haren kunar-bakin-wake biyu da Falasdinawa suka kai sun kashe 'yan Isra'ila 15, suka kuma raunata wasu masu yawa a Haifa, da unguwar kwace-ka-zauna ta Yahudawa ta Efrat dake kusa da Hebron.

Kungiyar Hamas tayi ikirarin kai harin bam na gidan abinci a garin Haifa.

A wani lamarin kuma, jami'an tsaron Isra'ila sun ce 'yan bindiga daga kudancin Lebanon sun bude wuta kan wata tashar sojojin Isra'ila a yankin gonakin nan na Shebaa da ake rikici kansu.

A ranar asabar, sojojin Isra'ila da askarawan Hezbollah na Lebanon sun yi musanyar wuta babu kama hannun yaro a wannan yankin.

XS
SM
MD
LG